<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>59</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Mun gode maka, Allahnmu,
 Domin maganar gaskiyarka,
 Umarninta ne haskenmu,
 Koyarwarta fitila ce.

[V2]
 2) Maganarka mai tsarki ce,
 Mun kafa bege cikinta,
 Maganarka duk gaskiya ce,
 Bari ta zauna a zuciyata.

[V3]
 3) Maganarka ce takobi,
 Takobi kuwa na Ruhunka,
 Ka sa ta soki zuciyarmu,
 Ta tsautar, har ma ta kwaƃe mu.

[V4]
 4) Ya Allah, buɗe zuciyarmu,
 Haskaka kuma duhunmu,
 Ka buɗe kuwa fahiminmu,
 Ka koya mana, Allahnmu.</lyrics>
<title>Mun Gode Maka, Allahnmu LW59</title>
</song>